TASHEN MACUKULE A MATSAYIN WASAN KWAIKWAYO NA MUSAMMAN A KASAR ZAZZAU

ABSTRACT
This thesis entitled “Tashen Macikule a Matsayin Wasan Kwaikwayo na Musamman a {asar Zazzau”, portrays „tashen macikule‟ as dramatic and also went ahead to indicate its uniqueness among other Hausa traditional drama. The study has successfully shows how „tashen macikule‟ differ from all kind of Hausa plays and even among its group of „wasannin tashe‟ by giving a critical out look of dramatic features that characterised all plays as drama and how the play „ tashe macukule‟ distinguishes itself among its group members(wasannin tashe).
At the end, the study was able to establish and confirm that the play was of zazzau origin and its uniqueness among other wasannin tashe in various grounds.


TSAKURE
Wannan bincike mai taken “Tashen Macikule a Matsayin Wasan Kwaikwayo na Musamman a {asar Zazzau”, ya yi }o}arin bayyana Tashen macikule ne a matsayin wasan kwaikwayo, sannan ya }ara da bayyana shi a matsayin wasan kwaikwayo na musamman. Binciken ya yi haka ne ta hanyar fito da yadda tashen macikule ya sha bamban da sauran wasannin kwaikwayo da kuma wasannin tashe.
A }arshe, binciken ya gano cewa, tashen macikule bazazzagin tashe ne, domin a zazzau a ka }age shi, sa~anin sauran wasannin tashe wa]anda ba wanda ya san lokaci da muhallin }ir}iransu. Haka kuma binciken ya tabbatar da kasancewarsa na musamman daga sauran wasannin tashe.


BABI NA [AYA : GABATARWA.
1.0       Shimfi]a:

Wasan tashe dai wani wasa ne da ke da tsawon tarihi wanda har ma ba a iya cewa ga takamaiman lokacin da aka fara gudanar da wasan ba. Haka kuma ba za a ce ga ainihin wanda ya fara gudanar da shi a }asar Hausan ba, wadda ita ce cibiyar da ake gudanar da wa]annan wasannin tashe. Wannan aiki zai mai da hankali kan tabbatar da kasancewar wasan tashe wasa ne na musamman.

Masana da manazarta wasan kwaikwayo irin su Yahaya(1978) da Abdullahi(1986) da Dangambo(1981) da Ogunbiyi (1981) da Bashir (2002) sun gudanar da bincike da dama a kan wannan nau‟in tashe a kan asalin tashe, da yanayinsa da nau‟o‟insa da rabe-rabensa dangane da jinsin taurari da jigoginsa da na dangantakarsa da rayuwar Bahaushe, da sauransu da dama.


1.1       Manufar Bincike

Kowane bincike da ]an Adam ya sa gaba a rayuwarsa, yana da manufa wadda ita ce take nuna abubuwan da za a bincika. Kamar yadda masu bincike suka bambanta, haka manufofinsu suka bambanta. Wannan kuwa ba sabon abu ba ne.

Tashe, wasan kwaikwayo ne wanda Hausawa suke yi a watan Azumi. Hanyoyin da ake bi don aiwatar da shi sun bambanta daga gari
zuwa gari. Alal misali, a kan sami „yan bambance-bambance tsakanin tashen da ake yi a Kano da kuma wanda ake yi a Zariya. Don haka, babbar manufar wannan bincike ita ce tabbatar da tashen macukule a matsayin wasan kwaikwayo na musamman a }asar Zazzau.

Haka kuma, kasancewar }asar Zazzau birnin ilimi, binciken zai fayyace tasirin addini a kan wasan tashen macukule.

Binciken zai nuna tasirin ba}in al‟adu a kan wasan tashen macukule a }asar Zazzau.

Haka kuma, binciken zai nuna bambance-bambancen da ke tsakanin tashen macukule da wasannin kwaikwayo „yan loto-loto irin su wasan gauta da wasan giwa-sha-laka da wasan kalankuwa da kuma na yau da kullum irin su wasan langa da wasan tirke da wasan „yar-tsana. Wa]annan bambance-bambance da ke tsakanin wa]ancan wasannin kwaikwayo da na wasannin tashe irinsu, Tsoho da Gemu da Ga Mairama ga Daudu da Tashen Macukule su za su tabbatar da wasan tashe a matsayin wasan kwaikwayo na musamman, tare da fayyace wasan tashe a matsayinsa na musamman a tsakanin „yan uwansa wasannin tashe ta hanyar yanayin Zubi ko Tsari da |adda kama ko kayan wasa da Taurari da Salo da Jigo.


1.2       Dalilin bincike:

Babban dalilin gudanar da wannan bincike shi ne tantancewa da adana wannan muhimmin wasan tashe wanda a iyaka sanin mai bincike babu wani bincike da aka gudanar a kan sa, ballantana a tantance matsayinsa, tare da warware }umshiyarsa a tsakanin sauran wasannin tashe.

Wani dalilin binciken shi ne na nuna asalin wasan macukule. Wannan aiki zai fayyace cewa ainihin wasan tashen macukule wasa ne mai asalin Zazzaganci.


1.3       Farfajiyar Bincike:

Nazarin tashe fage ne mai fa]i wanda ya }unshi siga da muhalli da jinsi da jigogi mabambanta da ke ]auke da al‟adun jama‟a daban daban daga ~angarorin }asar Hausa. Sai dai duk da haka, nahiyar ta yi tarayya da juna ta fuskar lokaci da muhalli da kuma taurarin gudanar da wasan tashe.

Wannan ne ya sa aka iyakance ko ta}aita muhallin binciken zuwa }asar Zazzau domin a sami damar gudanar da ingantaccen bincike da zai zamo abin alfahari kuma abin kwatance. Sannan a samar da jagora ga masu sha‟awar fa]a]a bincike a ~angaren.

Wannan aiki zai nazarci wasannin tashen macukulen da yara matasa kan gudanar da kuma tashen macukule na Audu Kwamandan Gwari.


Wannan aiki zai ta}aita ne daga lokacin samun „yancin kan Nijeriya zuwa yau.


1.4       Hasashen Bincike:

Wannan bincike na da hasashen tantance matsayi da mahimmancin wasan tashen a }asar Zazzau.

Shin ko akwai tasirin addinin musulunci a cikinsa?

Shin Wasan Macukule yana da wani tsari ne ko salo na musamman?

Shin ko Wasan Macukule da]a]]e ne kamar sauran wasannin tashe?

Shin ko akwai tasirin ba}in al‟adu  a cikin Wasan Macukule?

Shin ko Wasan tashen macukule zai iya zama wani fitaccen wasa a cikin wasannin tashe?


1.5       Mahimmancin Bincike:

Yin amanna da cewa dukkan wani aiki da ]an Adam kan gudanar a cikin harkokinsa na yau da kullum musamman a fagen ilmi na da muhimmanci irin nasa. Wannan aiki kamar sauran ayyukan masana da manazarta adabi yana da mahimmanci, kamar haka:

Tunanin irin rawar da al‟adu kan taka a fagen rainon yara da tarbiyarsu da irin tasirin ba}in al‟adu da tsoron ~acewar al‟adun, ya sa aka yun}ura wajen wannan bincike da nufin adana al‟adun da wasan tashen Macukule ya }unsa domin „yan baya.



Bahaushe mutum ne mai fasahar harshe da iya }ir}ira da kwaikwayo, wannan aiki zai tabbatar wa duniya ta hanyar amfani da wannan wasan tashe cewa bahaushe ba a baya yake ba wajen adana wa da rainon al‟ummarsa.

Ana fata ya zama wani kundin tarihin da ya taskace dangantakar Hausawa da Gwarawa.

Ya taimaka a magance }arancin litattafan da suka tarke wasannin kwaikwayo na gargajiya da hikimomin cikinsu a ]akunan karatu da makarantun da ake da su.

Zai zaburar da manazarta wajen za}ulo hikimomi da fasahar da ke jibge cikin wasannin gargajiya (tashe).

Manazarta Tarihi za su amfana da wannan aiki matu}a, masamman yadda wasan ya taskace wasu al‟amuran tarihi wa]anda suka faru a }asar Zazzau. Misali yadda ya taskace matsalar neman shari‟a a }asar Zazzau. Haka kuma da yadda ya taskace tarihin siyasar jihar Kano, misali rikicin jam‟iyar PRP tsakanin Gwamna Abubakar Rimi da Sabo Bakin Zuwo.


1.6       Hanyoyin Bincike

1.6.1 Ziyartar ]akunan karatu:

Yayin wannan bincike an ziyarci ]akunan karatu da nufin samun wasu bayanai ko sharhi kan tashe. Wasu littattafan ma na wasan kwaikwayo ne.


Haka kuma an duba kundayen bincike, wato na neman digiri tun daga na uku da na biyu da na ]aya kai harma na neman shedar takardar malanta mai daraja ta ]aya da nufin fahimtar gudunmuwar masana da almajiran Adabi a wannan fage na tashe musamman da nufin samun }arin haske kan yadda ake gudanar da wasan tashen macukule.

Yayin gudanar da bincike har-ila-yau an nazarci mujallu da }asidu da jaridu masu ]auke da bayanai masu ji~i da wasanin kwaikwayo da tashe da ma tashen macukule shi kansa.


1.6.2        Sauraron Kafafen ya]a Labarai:

Kafafen ya]a labarai na ]aya daga cikin mahimman hanyoyin da aka bi don gudanar da wannan bincike. A watan Azumi musamman da ce wa ya kai goma ga wata, a kan saurari gidajen Radiyon Tarayya na Kaduna da na Jihar Kaduna da Nagarta Radiyo da sauransu wa]anda kan sanya faya-fayan tashen su Audu Kwamandan Gwari da Mu‟azu Indagi da sauransu a lokacin tashe. Haka kuma an kalli gidajen talabijin na tarayya Kaduna da na Zariya.


1.6.3 Kallon Masu Yin Tashen Macukule:

Yayin yin wannan bincike, an kalli masu yin tashe a lokacin da suke gudanar da shi a lokuta da dama. Haka kuma an sami damar kallon masu yin tashen macukule. Misali: tashen macukule na Malam Audu [andun}ule
wani lebura mutumin Kano da na Sani [angaye wani almajirin makarantar Allo mutumin Unguwar Bala cikin gundumar Hunkuyi da sauransu da dama.


1.6.4       Hira da Jama’a:

Yayin gudanar da wannan bincike, an gana da dattawa wa]anda suka taka muhimmiyar rawa a zamanin da suke yara wajen aiwatar da tashe game da yadda suke gudanar da tashen a zamaninsu da kuma irin matsayin da al‟umma ta ba shi a jiya tare kuma da neman sanin yadda suke ganin matsayin tashen a yau.


1.7       Na]ewa:

A ta}aice, wannan babi ya yi bayanin muhallin wannan aiki da nufin samar da ingantaccen sakamako abin tun}aho. Binciken na da hasashen nuna wasan tashe a matsayin wasan kwaikwayon Hausa na musamman a Zariya.

A }arshe, wannan babin ya ambaci mahimmancin binciken da dalilin binciken. Har wa yau babin ya nuna duk hanyoyin da za a bi domin gudanar da ingantaccen aiki.

For more Hausa Projects click here
================================================================
Item Type: Project Material  |  Attribute: 135 pages  |  Chapters: 1-5
Format: MS Word  |  Price: N3,000  |  Delivery: Within 30Mins.
================================================================

Share:

No comments:

Post a Comment

Select Your Department

Featured Post

Reporting and discussing your findings

This page deals with the central part of the thesis, where you present the data that forms the basis of your investigation, shaped by the...

Followers