MATSAYIN HABAICI A ZANTUTTUKAN HIKIMAR HAUSA

ABSTRACT
The work examines the existence and various manifestations of innuendo (Habaici) in Hausa wise sayings. It also examines its various roles as a genre in Hausa oral literature. Consequently, it is observed that the Hausa’s use and exchange innuendoes in most parts of their lives that permeates communications, as well as in poetry, prose and drama. The work further elaborate on the relationship between innuendo and its counterparts like proverbs, epithets, etc. A cursory look on its stylistics pattern was also made.

TSAKURE
Wannan aiki ya yi nazarin Habaici a matsayinsa na wani vangare na zantuttukan hikimar Hausa. Habaici abu ne mai matuqar mihimmanci ga rayuwar Bahaushe wanda ya sanya Bahaushen yin amfani da shi a kusan dukkan vangarori na rayuwarsa da suka haxa da waqa da zube da wasan kwaikwayo da sauransu. Aikin bai tsaya a nan ba sai da ya faxaxa kan irin dangantakar da ke tsakanin habaici da sauran zantuttukan hikima na Hausa kamar su karin magana da kirari da sauransu. A qarshe kuma aikin ya yi tsokaci a kan irin salon da ake amfani da shi a wajen yin Habaici.

BABI NA XAYA: SHIMFIXA

1.0      Gabatarwa

Kowace al’umma ta duniya tana da hanyoyinta na zantuttukan hikima da take amfani da su a cikin harshenta don nuna gwaninta da kinaya da dabara da vad-da-bami a cikin harshen yayin da buqatar hakan ta samu.

Harshen Hausa cike yake da zantuttukan hikima na wanda za a iya cewa ana yin su ne ba kurum don nuna qwarewa da basirar sarrafa harshe ba, ana kuma yin amfani da su domin isar da saqo cikin nishaxi.

Bugu da qari duk wata qirqira ta zantuttukan hikima walau sabuwa ko tsohuwa duk ilahirin ma’anar da ta qunsa tana cikin harshen da wannan al’umma ke amfani da shi kamar yadda yake a harshen Hausa.

Ke nan harshen Hausa cike yake da zantuttukan hikima masu qayatarwa, kamar su habaici da karin magana da kirari da zambo da take da makamantansu, kamar yadda wannan bincike ya yi nazarin habaici a zantuttukan hikima na Hausawa.

Baya ga ado da bunqasa harshe da habaici ke yi a harshen Hausa babban abin dubawa shi ne irin saqon da yake isarwa ga al’umma da salailan da yake da shi da kuma irin yadda ake amfani da shi wajen gargaxi da huce haushi da mayar da martani da wajen faxakarwa, wani lokaci ma har da koyar da wasu abubuwa da suka shafi halin rayuwar yau da kullum.

1.1      Maqasudin Bincike

Habaici wani nau’i ne na zancen hikima da ake amfani da shi a nusar da mutum a fakaice. Yawanci habaici yakan qunshi kwatanta wasu abubuwa da nufin nuna gazawa ko raini ko mayar da martani ga wanda aka yi wa shi (Umar, 1980:24).

A wannan bincike an yi nazarin habaici a zantuttukan hikima na Hausawa, dangane da haka akwai matsaloli da aka ci karo da su kamar haka:-


-                    Guntayen zantuttukan hikima na Hausawa sun haxa da karin-magana da take da kirari da zambo da gatse da baqar-magana da shaguve da habaici da sauransu. A nan tambayar ita ce, yaya kowane xaya daga cikin su yake?

-                    Shin akwai wani abu habaici?

-                    Yaya salailansa su ke?

-                    Wane irin muhimmanci yake da shi ga al’umar Hausawa.

-                    Sa’annan shin habaicin na taka rawa dangane da abubuwan da suka shafi rayuwar Hausawa?

-                    Idan akwai, waxanne abubuwa ne?

For more Hausa Projects click here
================================================================
Item Type: Project Material  |  Attribute: 102 pages  |  Chapters: 1-5
Format: MS Word  |  Price: N3,000  |  Delivery: Within 30Mins.
================================================================

Share:

No comments:

Post a Comment

Select Your Department

Featured Post

Reporting and discussing your findings

This page deals with the central part of the thesis, where you present the data that forms the basis of your investigation, shaped by the...

Followers